Cikin shekaru biyar,barayi sun kashe sama da mutane 3000 a Zamfara – Yari


Gwamnan jihar Zamfara,Abdulaziz Yari ya ce barayi dake dauke da makamai sun kashe mutane 3,526 cikin shekaru biyar da suka wuce.

Yari na magana ne a wurin taron tattaunawa kan batun samar da tsaro a jihar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya,NAN taron ya samu halartar babban sifetan ƴansanda na kasa, Muhammad Adamu, shugabannin al’umma da kuma fulani da manoma.

Yari wanda ya samu wakilicin, Abdullahi Shinkafi sakataren gwamnatin jihar ya kuma ce kusan ƙauyuka 500 maharan suka lalata.

Ya kara da cewa sama da hekta 13,000 na gonaki ko dai aka lalata ko kuma suka zama basu da amfani saboda manoma basa iya noma a cikinsu.


Like it? Share with your friends!

1
90 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like