Chaina na shirin harba wa Taiwan makamai | Labarai | DWHukumomin Chaina sun kaddamar da gagarumin atisayen soji a ranar Alhamis a nisan kilomita 20 da kasar Taiwan, kuma Beijing na shirin harba makamai masu linzami da ka iya gittawa ta tsuburin. Sai dai hukumomin Taiwan suka ce za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin kare kansu daga abin da suka kira taba martabarsu ta zama kasa mai cikakken iko daga abokan gaba ba.

Hakan dai ta biyo bayan ziyarar kakakin majalisar wakilan Amirka, Nancy Pelosi, da ta kai wa Taiwan a ranar Laraba duk da gargadi da Chaina ta yi cewa idan har ‘yar siyasar ta Amirka ta ziyarci Taiwan din, za ta dauki mataki. 

Chaina dai ta jima tana daukar Taiwan a matsayin bangaren kasarta da ya fandare. Sai dai hukumomin Taiwan sun sha nuna kansu a matsayin kasa mai cikakken iko. 

 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg