Tuni Mahamat Idriss Deby da ke zama shugaban kasa na wucin gadi ya amince Firaminista Paraclet da ya rattaba hannu.

A nada ministoci 40 da kuma Sakatarori. A cikin wannan gwamnatin an sanya wasu tsoffin ‘yan adawa da gwamnatin Idriss Deby Itno, kamar Mahamat Ahmat Alhabbo a matsayin ministan Shari’a.

Sai dai madugun ‘yan adawa Saleh Kebzabo bai samu shiga gwamnatin ba, amma an sa sunayen mutune biyu daga cikin jam’iyarsa 

Kallabi tsakanin rawunan, mace daya tilo da ta tsaya takara na neman shugabancin kasar a zaben watan Afrilu, Madam Ladi Bayasinde ta samu matsayin ministan ilimi mai zurfi da bincike.