A cewar sanarwar da Labidi Ouoba jami’ar gwamnati wacce ta tsallake rijiya da baya a harin.Jami’ar ta kara da cewar maharan sun bi gida-gida suna cinna musu wuta duk wanda yai kokarin guduwa su harbe shi, da take nanata yadda ta gudu, ta ce Allah ne kawai ya sa kwananta ba su kare ba, amma a duk lokacin da suka shiga gari kai hari irin haka jami’an gwamnati suke fara nema, amma a wannan karon ba su yi ba. Wannan harin dai na zuwa ne mako guda bayan kisan wasu ‘yan jaridar kasar Spain biyu da wani jami’in alkinta muhalli na kasar Ireland a wani harin kwantar bauna da aka kai musu a lokacin da suke rangadin ‘yan farauta dadi.Rashin kayayyakin aiki ga dakarun sojin kasar na dakile yunkurinsu na yin fito na fito da maharan da ke da ala’ka da kungiyar Al-Qaida da kuma ta IS a lokuta da dama.