Buratai ya sake bude titin Maiduguri zuwa Damboa


Babban hafsan sojan kasan Najeriya, Tukur Yusuf Buratai a ranar Talata ya sake bude babban titin Maiduguri zuwa Damboa bayan da sojoji suka rufe shi tsawon watanni sha uku.

Buratai a lokacin bikin bude hanyar da aka gudanar a shingen bincike dake Molai a wajen birnin Maiduguri ya ce yanzu an bude hanyar domin amfanin motoci da fasinjoji dake zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Biu da kuma sauran garuruwa dake kusa.

Babban hafsan ya tabbatarwa da masu motoci da kuma farar hula dake bin hanyar samun kariya inda ya ce ya umarci kwamandodi da su bayar da tsaro ga kowa da kowa dake amfani da hanyar.

Idan za a iya tunawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya roki a sake bude hanyar. Ya yi rokon ne lokacin da ya kai wa ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi ziyara a Abuja.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like