Buni ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC


An ruguje shugabancin jam’iyar APC na kasa dake karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.

Victor Giadom, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar shi ne ya sanar da haka a wurin taron shugabannin jam’iyar na kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Gwamnan jihar Yobe,Mai Mala Buni shi ne aka rantsar a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar.

Ministan shari’a, Abubakar Malami shi ne ya bashi rantsuwar kama aiki.

Sai dai tsofaffin shugabannin da aka sauke sun yi watsi da sakamakon taron na yau inda suka ce haramtacce ne.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like