BUHARIN BORNO YA TARO FADA MAI ZAFI


Rahoton Datti Assalafiy


Maigirma gwamnan jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya nuna yatsa wa kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba “Non Governmental Organisations” (NGOs) da suke aikin bada agaji a fadin jihar Borno, yace dole su gabatar da ayyukansu karkashin kulawar gwamnatin jihar Borno imba haka ba su fice daga jihar

Jama’a kun san dalilin da yasa Maigirma gwamna ya gindaya musu wannan ka’idar? dalilin shine su wadannan kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba, wanda nake cewa kungiyoyin sharri suna cin amanar tsaron Nigeria ta hanyar tallafawa ayyukan ta’addancin Boko Haram ta bayan fage, tare kuma da baiwa ‘yan ta’addan mafaka da yin jinya na magani garesu ‘yan ta’addan

Mutanene suka zama annabo ‘yan ta’adda, suka gudu daga gari sukaje suka buya a jeji, aikinsu kenan kashe mutane, sai aka samu wasu kungiyoyin sharri sukazo suka mamaye muku gari, suna bin mutanen can dake kashe ku cikin jeji suna basu agaji ta bayan fage, don girman Allah wace kasa ce a duniya zata yarda da wannan cin amanar?

Idan ba’a manta ba, watannin baya rundinar Sojin Nigeria OPERATION LAFIYA DOLE sai da ta kama daya daga cikin wadannan kungiyoyin sharri da suka mamaye jihar Borno da hannu dumu-dumu suna tallafawa ‘yan ta’adda, rundinar sojin ba ta yi kasa a gwiwa ba ta dakatar da kungiyar, amma ba’a samu kwana guda ba da dakatarwan aka tilasta rundinar sojin ta janye dakatarwan da ta yiwa kungiyar, saboda yadda sukayi karfi

Har ila yau, a shekaran da ta gabata ne, Maigirma Ministan tsaron Nigeria Malam Mansur Dan Ali ya fito ya sanarwa duniya cewa kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba (NGOs) da suka mamaye jihar Borno suna taimakon ‘yan ta’adda, kuma sun mayar da ta’addancin hanyar neman kudi, basa kaunar a kawo karshen ayyukan ta’addanci saboda kudin da suke samu, ku ziyarci BBC Hausa zaku samu bayanin

Don Allah duk wanda bai san ayyukan sirri na wadannan kungiyoyin sharri ba, ya ziyarci shafina na Facebook mai sunan


Like it? Share with your friends!

1
57 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like