Buhari zai turawa majalisar dattawa sunayen ministoci a cikin wannan makon


Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce majalisar zata karbi sunayen mutanen da shugaban kasa Muhammad Buhari zai naɗa ministoci kafin karshen makon da muke ciki.

Lawan ya fadi haka ne a zauren majalisar a ranar Laraba bayan da sanata Albert Bassey daga jihar Akwa Ibom ya taso da batun.

Bassey ya ce akwai bukatar Lawan ya shawarci Buhari ya mika sunayen tunda nan ba dadewa ba majalisar zata tafi hutun shekara.

“Idan har zamu tafi hutu nan da sati biyu kamata yayi ace yanzu sunayen mutanen da aka zaba su zama ministoci yana gaban mu,” a cewar sanatan.

Da yake mayar da martani Lawan ya ce bangaren zartarwa na aiki tukuru wajen ganin sun turawa majalisar jerin sunayen.

“Ina tunanin kafin wannan satin yakare zamu iya karbar sunayen,” ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like