Buhari zai tafi aikin Umrah kasar Saudiyya


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amsa gayyatar da Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz ya yi masa ta zuwa yin aikin Umrah.

Amsa gayyatar na nufin shugaban kasar tare da wasu masu taimaka masa za su kama hanyar zuwa kasa mai tsarki ranar Alhamis 16 ga watan Mayu.

Ana san ran shugaba Buhari zai dawo gida ranar Talata 21 ga watan Mayu.

Har ila yau shugaban kasa zai sake komawa kasar ta Saudiyya domin halartar taron kungiyar kasashe musulmi ta OIC da za a gudanar ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni.


Like it? Share with your friends!

-1
62 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like