Buhari zai samu kuri’a miliyan 2.5 a jihar Katsina – Masari


Gwamnan jihar Katsina,Aminu Bello Masari, ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari zai sami akalla kuri’a miliyan 2.5 daga jihar a shekarar 2019.

Masari ya fadi haka bayan da ya gana da shugaban kasa Muhammad Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Alhamis.

Buhari wanda ya fito daga jihar ya samu ƙuri’u 1,345,441 a zaben shekarar 2015, jihar tana da mutane miliyan 2,827,943 da suka yi rijistar zabe, a wancan lokacin.

Ya zuwa watan Agusta hukumar zabe ta kasa, INEC ta bayyana cewa karin mutane 329,257 sabbi da ta yiwa rijista.

Da yake magana da masu dauko rahoto daga fadar shugaban kasa, gwamnan na Katsina ya ce mutanen jihar a shirye suke su kara yawan ƙuri’un da suka bawa shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

“Mutanen Katsina suna bayan shugaban kasa Muhammad Buhari ɗari bisa ɗari kuma za su cigaba da goya masa baya har bayan kammala zaben 2019,” ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like