Buhari Zai Sake Tafiya London Don Duba Lafiyarsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi London a ranar Juma’a don duba lafiyarsa, fadar gwamnatin kasar ta bayyana.

“Buhari zai tafi London da ke kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni 2021, don komawa ya sake bibiyar lafiyarsa.” Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta ce.

Shugaban zai dawo a mako na biyu cikin watan Yulin da ke tafe a cewar Adesina.

A watan Maris Buhari ya kai ziyara birnin na London inda ya je duba lafiyarsa, ya kuma kwashe kusan mako biyu a can kafin ya koma gida.

Wannan ita ce ziyara ta biyu cikin wata kusan uku da shugaban zai je London don ganin likita.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.