Buhari zai halarci taron ECOWAS a Burkina Faso


Shugaban kasa Muhammad Buhari zai bar birnin tarayya Abuja ranar Asabar ya zuwa birnin Ouagadugu na kasar Burkina Faso domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS.

Taron na musamman da za a gudanar zai mayar da hankali kan yaki da ta’addanci.

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma sun kira taron ne domin sake duba matakai daban-daban da suka dauka a baya da kuma sake shata wasu tsare-tsare da za su hana barazanar tsaro dake cigaba da karuwa a yankin

A yayin ziyarar shugaban kasar zai samu rakiyar gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello na jihar Abia,Okezie Ikpeazu da kuma na jihar Ogun,Dapo Abiodun.

Sauran yan tawagar shugaban kasar sun hada da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da na tsaro Bashir Salihi Magashi.

Har ila yau tawagar ta kunshi mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da kuma shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya, Ahmed Rufa’i.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like