Buhari zai gabatarwa majalisa kasafin kudin shekarar 2019 ranar Laraba


Shugaban kasa Muhammad Buhari zai gabatarwa da majalisar ƙasa kasafin kudin shekarar 2019 ranar Laraba.

An bayyana haka ne cikin wata wasika da kakakin majalisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis.

Bayan karanta wasikar ne wasu daga cikin yan majalisar suka yi barazanar kauracewa zaman majalisar na ranar da shugaban kasar zai gabatar da kasafin kan kalaman da ministan kudi da tsare-tsare Udom Udoma ya yi.

A karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba Udoma ya fadawa yan jaridu cewa bangaren gwamnati ya kammala aiki akan kasafin kudin amma kuma majalisar ta gaza saka ranar da shugaban kasa zai gabatar da kasafin.

Dan majalisa Chika Adamu ya bayyana cewa Udoma ya yi karya inda ya yi kira ga abokan aikinsa da su bukaci ya basu hakuri.


Like it? Share with your friends!

-1
88 shares, -1 points

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *damage ai yan majalisa bakaunar talakawa sukeyiba donhaka Allah yakarawa baba BUHARI karhin gwiwa alfarmar annabi.

You may also like