Buhari ya ziyarci Kaduna kan rikicin dake faruwa a jihar


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ziyarci jihar Kaduna inda ya gana da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addini kan rikicin dake faruwa a jihar.

Taron ya gudane a rufaffen wurin wasanni dake Murtala Square a Kaduna.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, sakataren kungiyar Jama’atul Nasril Islam,Dr Khalid Aliyu, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, George Dodo da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

A yan kwanakin nan jihar Kaduna ta sha fama da rikicin har ta kai ga an sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24.

Rikicin dai ya samo asaline daga garin Kasuwar Magani a karamar hukumar Kajuru inda aka kashe mutane 55 a wani rikici da har ya zuwa yanzu ba a san musabbabin faruwarsa.

Daga nan kuma rikici ya bazu ya zuwa garin Kaduna.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like