Buhari ya ziyarci garuruwan da rikice rikicen ta’addanci ya shafa a jihar Katsina


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wata ziyarar jajantawa ga al’ummomin kananan hukumomin da suke fama da matsalar tsaro da hare haren ta’addanci, Inda ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati tana daukar duk matakan da suka kamata kuma da yardar Allah an kusa kawo karshen wannan matsala, abinda ake bukata daga al’umma shi ne dagewa da addu’o’in Allah ya kawo mana dauki ya kuma bamu zaman lafiya mai dorewa.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi godiya tare da jinjina ga shugaba Muhammadu Buhari bisa irin kokarin da yake na tsare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar nan dama jihar Katsina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a garin Batsari lokacin da Buhari ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummomin kananan hukumomin da suke fama da matsalar tsaro da hare haren ta’addanci, Ya kuma kara da cewar gwamnatin jiha ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bada duk gudummawa da tallafin da jami’an tsaro suke bukata don ganin an kawo karshen wannan ibtila’in.

Shima mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Dakta Abdulmumin Kabir Usman shi kuwa kira ya yi ga al’umma da su so juna kuma su sa ido akan duk al’amurran da suka shafe su musamman na tsaro tare da bada sahihan bayanai a inda ya kamata domin saukaka wa jami’an tsaro hanyar sauke nauyin da ya rataya kansu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like