Buhari ya yi waya da Sarki Salman na Saudiya


Sarkin Saudiya, Salman Ibn Abdulaziz Al Saud ya kira shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari ta wayar tarho a ranar Alhamis domin tattaunawa kan wasu batutuwa da suka shafi kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency ne ya fitar da labarin rahoton tattaunawar shugabannin biyu.

A cewar kafar yada labarai ta Saudi Gazette shugabannin biyu sun duba batun wasu alakoki dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan ne karo na biyu da sarkin yake ganawa da shugaba Buhari ta wayar tarho.

A cikin watan Agusta ne ya gana da Buhari ta wayar tarho a kokarin da suka yi na dai-dai ta farashin danyen mai a kasuwar duniya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like