BUHARI YA YI WATSI DA MU BAYAN YA SAMU NASARA – Kungiyar ‘Yan Ga-Ni-Kashe-Nin Buhari


Kungiyar magoya bayan Buhari na ga-ni-kashe-ni ta koka kan cewa Shugaban kasa Muhuhammadu Buhari ya yi watsi da ita bayan samun nasarar zaben 2015.

Shugaban kungiyar, Musa Inuwa, ya gaya wa manema labarai a jihar Kano cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai masu sakayyar kokari da tashi-fadin da suka sha ba tun daga lokacin da ya fara takarar kujerar shugaban kasa a 2003, har ya zuwa lokacin da ya samu nasararsa a 2015.

Inuwa ya bayyana cewar sun yi gumurzu cikin sadaukarwa a gurin kamfe din Shugaba Buhari. Ya ce har kulle su a kurkukun Karshi an yi sakamakon zanga-zangar nuna goyon bayan Buhari da suka shiga a 2007.

Ya kara da fadin cewa a lokacin da aka tare tawagar Shugaba Buharin a wancan lokacin, aka hana shi da jerin tawagarsa shiga garin Daura, su ne dai ‘yan ga-ni-kashe-nin da suka buda tare da fafatawa har sai da suka buda masa hanya ya shige.

Inuwa ya yi zargin cewa shugaban kasar ya kewaye kansa da mutanen da ba sa kaunarsa da gaskiya. Mutanen da ba su tsoma hannu a cikin fadi-tashin siyasarsa ba amma su ne yanzu suke sharbar romo a gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun yi tsammanin Buhari zai yi aiki tukuru fiye da abin da yake aiwatarwa a yanzu, musamman a fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya da lantarki. Sai dai ba wani abin arziki a kasa.


Like it? Share with your friends!

1
102 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like