Buhari ya yi magana da yan kungiyar Super Eagle


Shugaban kasa Muhammad ya yi magana da tawagar yan wasan ƙwallon ƙafar Super Eagle gabanin wasan da za su buga na yau da kasar Crotia.

Shugaban ya tabbatarwa da yan wasan goyon bayan da yan kasa suke musu.

Shugaban ya kuma yiwa yan wasan fatan alheri a madadin dukkanin yan Najeriya miliyan 180.

Shugaban ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Na yi magana da yan wasan kungiyar Super Eagle gabanin wasansu na farko da kasar Crotia a gasar cin Kofin Duniya inda na tabbatar musu da cikakken goyon bayan kasarnan garesu,” ya ce.

Najeriya ta kasance a rukunin D dake kunshe da kasashen Argentina, Crotia da kuma Iceland.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like