Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zabe


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zabe da ya yi a karo na biyu.

Hukumar zabe ta INEC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba bayan da ya samu kuri’a 406,222 inda ya kayar da Musa Wada na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 189,704.

Buhari ya shawarci gwamnan da ya dora akan harsashi ginin da ya fara na inganta rayuwar mutanen jihar.

Har ila yau shugaban kasa ya yabawa jami’an tsaro kan rawar da su taka ta ganin anyi zabe lafiya.

Kungiyoyi da dama da suka sanya idanu a zaben sun yi kira da a soke zaben saboda yadda yake cike da rikici.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like