Buhari ya tashi zuwa kasar Chadi


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tashi daga filin jirgin saman Abuja da safiyar yau ya zuwa birnin N’Djamena na kasar Chadi.

Buhari zai jagoranci taron shugabannin kasashen dake kewaye da tafkin Chadi domin tattauna yanayin tsaro a yankin.

Taron na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke zafafa kai hare-hare a yankin.

Kasa da makonni biyu da suka wuce ne bangaren kungiyar ta Boko Haram dake biyayya ga kungiyar ISIS suka kai wani mummunan hari kan sansanin sojan Najeriya dake Metele inda suka kashe sojoji da dama.

A wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta bakin, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ta ce sojoji 39 rundunar ta rasa a harin da aka kai sansanin.


Like it? Share with your friends!

2
53 shares, 2 points

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. Allah ya dawo mana da shugabanmu lafiya, ya bashi nasara da yakin danyake da yan ta,adda, sai Buhari insha Allah 2019!

You may also like