Buhari Ya Tafi Birnin Kigali
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi Kigali, babban birnin kasar Rwanda domin halartar taron koli na kungiyar kasashen da Ingila ta rena.

Taron zai mayar da hankali ne wajen duba fannonin da za a bunkasa kasashe 54 da suka kasance mambobi a kungiyar kasashen da Ingila ta rena, wanda ake ya wa lakabi da CHOGOM a takaice.

Shugaban na Najeriya zai hadu da sauran takwarorinsa da suka fito daga nahiyar Afirka, Asiya, Turai da kuma yankin Amurka don tattauna batutuwan da za su shafi rayuwar sama da mutum biliyan biyu da ke kasashe 54.

Taron kolin zai gudana ne a karo na 26 wanda aka yi masa taken, “Samar da makoma daya: hadin kai, kirkire-kirkire da samar da ci gaba.”

Ana kuma sa ran shugabannin kasashen za su kara jaddada mubaya’arsu ga kudurorin da kungiyar ta sa gaba, wadanda suka shafi batutuwan dimokradiyya, ‘yancin dan adam, bin doka, da harkokin kasuwanci.

Batutuwan da za a fi mayar da hankali akansu sun hada da annobar COVID-19 da yadda ta shafi tattalin arziki, sauyin yanayi, neman rangwamen bashi, rage talauci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Za a bude taron a hukumance a ranar 24 ga Yuni, a kuma ranar Lahadi ake sa ran Shugaba Buhari zai koma Najeriya.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg