Buhari Ya Tabbatar Da Mukaddashin Sufeto Janar Na Kasa


A zaman majalisar tsaro ta kasa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a yau Alhamis a fadar gwamnatin tarayya, Buhari ya amince da mukaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu a matsayin Sufeto Janar na kasa baki daya (IGP).

Wannan na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran gwamnonin Najeriya ya gamsu da salon yadda Sufeto Janar na ‘yan Sandan ya ke gudanar da hukumar ‘yan sandan.

Taron wanda ya samu halartan gwamnonin jihohi 36 tare da hukumar kula da ‘yan sanda karkashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Misliu Smith.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like