Buhari ya sauya sunan filin wasa na kasa dake Abuja ya zuwa sunan MKO Abiola


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauya sunan babban filin wasa na kasa dake Abuja ya zuwa Filin Wasa na MKO Abiola mutumin da ake tunanin ya lashe zaben 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a dandalin Eagle Square dake Abuja wajen bikin murnar Ranar Dimakwaradiya.

A shekarar da ta gabata ne shugaban kasar ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimakwaradiya domin girmama marigayi Abiola wanda ya bawa babbar lambo ta kasa bayan mutuwarsa.

Abiola ya lashe zaben shugaban kasa na 1993 amma gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben.


Like it? Share with your friends!

-1
93 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like