Buhari ya sake Nada farfesa Mohmoud  Yakubu a matsayin shugaban INEC karo na biyu

Shugaban ‘Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a karo na biyu a matsayin shugaban hukumar.

A cikin wasikar da shugaban ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Shugaban ya ce bisa tanadin sashi na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya, 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), “Ina farin cikin da tabbatar da majalisar dattijai, nadin Farfesa Mahmood Yakubu don nada shi a matsayin Shugaban, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu kuma na karshe. ”

Shugaba Buhari ya fara nada Farfesa Yakubu a watan Nuwamba na shekarar 2015.

Wanan jawabin Yana kunshe a sanarwa da Mashawarci na musamman ga shugaban Kasa A kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar.