Buhari ya nesanta kansa da shirin magudin zaben gwamna a Kano


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nesanta kansa daga labaran da wasu suke yadawa dake cewa shugaban kasar ya bayar da umarnin a soke sakamakon zaben wasu kananan hukumomin jihar Kano.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu.

“Shugaban kasa Buhari bai bayar da wani umarni ba da a sauya sakamakon wasu kananan hukumomi ba a Kano.yanzu haka yana Daura bai gana da kowa ba ko kuma waya,” a cewar Shehu.

Shehu ya shawarci masu yada wannan karyar da suyi wa Allah su dena.

Dantakarar jam’iyar PDP,Abba Kabir Yusuf shine ke kan gaba a sakamakon da aka bayyana na kananan hukumomin 43.


Like it? Share with your friends!

-1
78 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like