Buhari Ya Nada Sulaiman Hassan A Matsayin Ministan Muhalli


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sulaiman Hassan a matsayin sabon ministan muhalli.

Kafin wannan sabon matsayin, Sulaiman Hassan shi ne karamin ministan makamashi, ayyuka da gidaje na kasar nan.

An ba shi sabon matsayin na ministan muhalli sakamakon murabus din da karamin ministan muhalli, Ibrahim Usman Jibril yayi saboda nadin sarautar Sarkin Nasarawa da aka masa a jiharsa ta Nasarawa.

A cikin wani jawabi da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya gabatar ya ce shugaban kasa ya sanar da nadin Sulaiman Hassan din a jiya Laraba.


Like it? Share with your friends!

-1
76 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like