Buhari ya ki sanya hannu akan dokar zabe


Shugaban kasa Muhammad Buhari yaki yarda ya rattaba hannu kan gyaran dokar zabe da majalisun kasa suka yi.

Ita Enang mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan majalisar dattawa ya ce shugaban kasar ya sanarwa da majalisun kasa matakin da ya yanke.

Amma Enang yaki yarda ya yi cikakken bayani kan dalilan da suka sanya shugaban kasar yaki rattaba hannu akan dokar kamar yadda ya yi cikkaken bayani kan sanya hannun da shugaban kasar ya yi akan gyaran dokar jami’ar karatu daga gida wato National Open University of Nigeria.

“Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dauki matakin da yace kan gyaran dokar zabe ta shekara 2018 kamar yadda kundin tsarin mulki shekarar 1999 ya bashi iko kuma tuni ya sanar da majalisar dattawa da kuma ta wakilai kamar yadda doka ta tanada,” ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like