An gabatar wa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wayar salula ta farko da kasar ta kirkira.

Ministan kasuwanci da saka hannayen jari a kasar Adenyiyi Adebayo ne ya gabatarwa da Buhari wayar wacce ake kira ITF wacce kirar Android ce.

A kwanakin baya hukumomin kasar suka bayyana cewa, Najeriyar na shirin kaddamar da waya wacce aka kera a kasar hade katin waya na sim.

Shugaba Buhari (hagu) da Minista Adebayo (Facebook/ Bashir Ahmad)

Shugaba Buhari (hagu) da Minista Adebayo (Facebook/ Bashir Ahmad)

Yayin gabatar da wayar gabanin a fara taron majalisar zartarwar da ake yi mako-mako, Adebayo ya ce cibiyar bincike kan kayan laturoni na hukumar koyar da makamar aiki ta ITF ne ya kirkiri wayar.

“In mai farin cikin gabatarwa da shugaban kasa wannan waya.” Adebayo ya ce, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Hakan na nufin Najeriya, mai yawan jama’a kusan miliyan 200, ta shiga jerin kasashen da ke hada wayar salula a duniya.