Shugaban kasa Muhammad Buhari, ranar Juma’a , ya karbi bakuncin shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa shugabar ta Germany wacce take kammala ziyarar da take a wasu kasashen Afirka ta yamma uku, ta isa fadar Aso Rock da misalin ƙarfe 10:02 na safe.
Shugaban kasa Buhari wanda ya tarbi shugabar kasar ta Germany a farfajiyar fadar Aso Rock, ya gabatar mata da wasu daga cikin yan majalisarsa da kuma masu taimaka masa kafin su shiga wata ganawar sirri da za su tattauna batutuwa da za su amfani Najeriya da Germany.
Merkel, na zangonta na karshe a ziyarar kwanaki uku da take kasashen, Senegal , Ghana da kuma Najeriya.