Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da shirin rabawa matasa kayayyakin dogaro da kai.

Ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan cigaban matasa,Mallam Nasiru Adahma shi ne ya kirkiro shirin da ake kira P-YES wato Presidential Youth Empowerment Scheme.

Za a tallafawa matasa 774,000 a duk fadin kasarnan wato kusan matasa 1000 kenan daga kowace karamar hukuma.