Buhari ya kaddamar da asibitin sojojin sama a Daura


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da asibitin sojan sama dake Daura jihar Katsina.

Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta zuba kudade makudai a fannin kiwo lafiya.

Har ila yau ya kara da cewa gwamnatin ta samu nasarar shawo kan wasu cututtuka dake da alaka da kisan kananan yara da kuma mata masu juna biyu.

Ya yin bikin shugaban kasar na tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da kuma Aminu Bello Masari na jihar Katsina.


Like it? Share with your friends!

2
69 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like