Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Shimfida Layin Dogo Daga Kano Zuwa KadunaYau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kai ziyarar aiki Kano, jiha mafi yawan jamaa a kasar.

A yayin ziyarar, shugaban ya aza harsashin aikin gina layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna wanda zai kasance ci gaba ne na wanda ya taso daga Abuja zuwa Kano.

Kazalika, shugaban ya bude hanyar gadar sama da gwamnati jihar Kano ta gina akan mahadar titinan Zoo Road da Zaria Road a cikin birnin Kano.

Shirye shiryen tartar shugaba Buhari

Shirye shiryen tartar shugaba Buhari

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da kusoshin gwamnati da kuma ministan sufuri Rotimi Ameachi da sauran mukarraban gwamnatinn tarayya ne suka tarbi shugaban wanda ya sauka a Kano da karfe goma na safe agogon Najeriya.

Bayan aza harsashin gina layin dogon, an tsara shugaba Buhari zai kai ziyarar ban girma ga mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Tuni dai jami’an tsaro suka tare manyan titinan Kano, musamman wuraren da aka tsara ayarin shugaban zai ratsa, alamarin da ya zefa Jama’a cikin mawuyacin hali wajen zirga-zirga saboda cunkoson ababen hawa.

Baki a wajen taron bude layin dogo

Baki a wajen taron bude layin dogo

Galibin Jama’a dai a Kano ba su da masaniya dangane da ziyarar shugaban, la’akkari da cewa, hukumomi a Kano ba su kwarmata ziyarar ba.

Fadar shugaban kasar ta ce daga Kano, shugaban zai wuce jihar Katsina inda zai kaddamar da dam din Zobe da hanyar Dutsinma/ Tsakiya mai tsawon kilomita 50.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.