Buhari ya isa Daura domin yin rijistar katin jam’iyar APC


Shugaban kasa, Muhammad Buhari a ranar Juma’a ya isa mahaifarsa ta Daura dake jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina,Aminu Bello Masari shi ne ya tarbi shugaban kasar a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina gabanin ya wuce zuwa Daura.

Duk da cewa Masari ya ce shugaban kasa na ziyara ne ta kashin kai kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ce shugaban kasar zai bi sawun dubban yan jam’iyar APC domin a asubunta masa katinsa a mazabarsa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

You may also like