Buhari ya gana da zaɓaɓɓen shugaban kasar Guinea-Bissau


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya gana da,Umaro Muhktar Sissoco Embalo sabon zaɓaɓɓen shugaban kasar Guinea.Bissau a fadar Aso Rock dake Abuja.

Sabon shugaban kasar ya zo Najeriya ne domin yin godiya kan taimako da kuma gudunmawar Najeriya ta taka a zaben da ya bashi nasara.

Buhari ya ya yabawa shugaban kasar mai barin gado, José Mário Vaz, wanda shima yayi takara a zaɓen kan yadda ya amince da sakamakon zagaye na biyu na zaben da ya bawa Embalo nasara.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like