Buhari ya gana da shugabannin majalisar koli ta addinin Musulunci


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya gana da shugabannin majalisar koli ta addinin musulunci NSCIA karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Ganawar da ta gudana a fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja ta kuma samu halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran waɗanda suka halarci ganawar sun hada da ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad,na harkokin cikin gida,Rauf Aregbesola da Babagana Monguno mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Har ila yau akwai mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar a ganawar.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan abin da ganawar ta kunsa sai dai ana sa ran yiwa yan jaridu bayani kan batutuwan da aka tattauna.


Like it? Share with your friends!

1

You may also like