Buhari ya gana da shugaban INEC


Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya jagoranci wasu kwamishinonin hukumar ya zuwa fadar Aso Rock dake Abuja.Abubakar Nahuche,Okechukwu Ibeano, May Agbamuche-Mbu da kuma Ahmad Muazu na daga cikin kwamishinonin hukumar na kasa da suka bi Yakubu wajen ganawar da shugaban kasa, Muhammad Buhari.Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Yusuf Magaji Bichi, babban sifetan yan sanda, Muhammad Adamu da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Mallam Abba Kyari suma sun halarci ganawar.Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce shugaban hukumar ta INEC ya yi wa Buhari jawabi kan yadda zaben 2019 ya gudana da kuma zabukan da aka gudanar a bayansa.Ana sa jawabin shugaba, Buhari ya yi kira ga hukumar ta INEC da ta yi adalci a zabukan cike gurbi da zata gudanar a mazabu daban-daban biyo bayan hukuncin kotuna.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like