Buhari ya gana da sarakunan gargajiya na jihar Kogi


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya gana da majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kogi dake karkashin shugabancin Attah na Igala.Masu rike da sarautun gargajiya sun gana da shugaban kasar a fadar Aso Rock dake Abuja karkashin jagorancin gwamnan jihar, Yahaya Bello.

Ya yin ziyarar sarakunan sun fadawa shugaban kasa cewar basu gamsu da mukamin karamin minista da aka bawa jihar ba a zangon mulkin Buhari na farko.

A cewar su ya kamata a daga darajarsu a majalisar zartarwa ta tarayya inda suka bukaci a bawa jihar mukamin ministan kudi.

Har ila yau sun nemi shugaban kasa Muhammad Buhari ya goyi bayan takarar gwamnan jihar Yahaya Bello a zango na biyu.


Like it? Share with your friends!

1
71 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like