Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya gana da Amina Muhammad mataimakiyar shugaban Majalisar Dinkin Duniya a fadar Aso Rock dake Abuja.

Har ila yau Amina Muhammadta gana da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Da take wa yan jaridu jawabi,Amina ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta damu matuka da irin barnar da ta biyo bayan zanga-zangar EndSARS da matasa suka gudanar.