Buhari ya dawo gida bayan shafe kwanaki biyar a kasar Saudiyya


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Najeriya ranar Talata bayan da ya kwashe kwanaki biyar a kasar Saudiyya inda ya gabatar da aikin umara.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, jirgin dake dauke da shugaban ƙasar da kuma yan tawagarsa wanda ya taso daga bangaren ta shi da saukar shugabanni dake filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da misalin karfe biyu na rana ya kuma sauka a sashen sauka da tashin shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 06:34.

Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ministan birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello,mai rikon mukamin babban sifetan ƴansanda na kasa, Muhammad Adamu da kuma sauran manyan jami’an gwamnati na daga cikin wadanda suke kasance a filin jirgin domin tarbar shugaban.

Ya yin da yake can kasa mai tsarki shugaban kasar ya gudanar da aikin umara tare da maidakinsa,Aisha Buhari da kuma wasu masu taimaka masa.

Har ila yau shugaban ya yi wani taron buda baki da jagoran jam’iyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu da kuma wasu fitattun yan Najeriya.

Sauran wadanda suka halarci taron shanruwan sun hada da mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma sarakin Kazaure,Hussaini Adamu.


Like it? Share with your friends!

1
78 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like