Buhari ya dakatar da shugabar ma’aikata,Oyo-Ita


A wani abu mai cike da mamaki shugaban kasa, Muhammad Buhari ya dakatar da shugabar ma’aikata ta tarayya,Winfred Oyo-Ita daga bakin aiki.

Haka kuma shugaban kasar ya ayyana sunan, Folashade Yemi-Esan a matsayin shugabar ma’aikata ta riko.

Oyo-Ita na fuskantar bincike daga hukumar EFCC kan zargin badakalar kwangila da ta kai biliyan ₦3.

A kwanakin baya ta mikawa shugaba kasar takardar barin aiki amma yaki amincewa da murabus din nata.

Hukumar yaki da cin hancin ta gayyace ta a kwanakin baya inda ta amsa tambayoyi kan zargin da ake mata na yin amfani da wasu kamfanoni, wajen samawa kanta kwangila lokacin da take rike da mukamin babbar sakatariya gabanin shugaba Buhari ya nada ta shugabar ma’aikata.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like