Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya jinjinawa Najeriya saboda matakin da ta dauka na haramta Twitter a kasar.

Trump ya kuma yi kira ga sauran kasashen duniya da su yi koyi da Najeriyar.

A makon da ya gabata Twitter ya goge wani sakon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya ce ya saba ka’idar kamfanin.

A martanin da suka mayar, hukumomin kasar sun haramta amfani da shafin sada zumuntar a kasar, wanda ke da miliyoyin mabiya a Najeriyar.

“Ina taya Najeriya murna, wacce ta dauki matakin hana amfani da Twitter, saboda ya (dakatar) da shugabanta. Ya kamata wasu karin kasashe su ma su haramta Twitter da Facebook, saboda suna hana ruwa gudu wajen fadin albarkacin baki.” Wata sanarwa da Trump ya fitar da maraicin ranar Talata ta ce.

A farkon shekarar nan, Twitter ya haramtawa Trump amfani da shafin, saboda abinda ya kira take ka’idarsa da ya yi, ta hanyar wallafa kalaman da ka iya ta da hatsaniya, lamarin da bai yi wa Trump da magoya bayansa dadi ba.

Trump ya yi ta wallafa kalamai da ke zargin an tafka magudi a zaben 2020, bayan kaye da ya sha a hannun Shugaba Joe Biden, ikirarin da bayanai suka nuna ba su da tushe.

“Waye Twitter da zai rika fayyace abu mai kyau da mara kyau, idan shi kansa, ba ya yin abu mai kyau” Trump ya ce cikin sanarawar.

Amurka da wasu kasashen nahiyar turai da dama, sun soki matakin da Najeriyar ta dauka na rufe dandalin na Twitter.

Hukumomin kasar sun ce sun dauki matakin ne saboda abinda ake wallafawa a shafin na Twitter na barazana ga zaman lafiyar kasar.

Sama da mutum miliyan 39 na amfani da shafin na Twitter a Najeriya kamar yadda kididdigar kungiyar NOI mai sa ido kan shafukan sada zumunta ta wallafa.