Buhari ya bayyana dalilin rufe iyakar Najeriya da Benin


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce Najeriya ta rufe kan iyakarta da Benin ta mashigar Seme dake Lagos domin dakile ayyukan masu fasa kaurin shinkafa.

Kwanaki takwas kenan da mashigar take a rufe kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa mashigar ta Seme za ta shafe tsawon kwanaki 28 a rufe.

Da yake magana lokacin da yake ganawa da Patrice Talon takwararsa na jamhuriyar Benin a wurin taron cigaban ƙasashen Nahiyar Afirka da ake yi a birnin Yokohama na kasar Japan. Buhari ya ce fasa kwaurin na kawo barazana ga tsare-tsarensa a fannin noma.

A cewar Femi Adesina mai magana da yawun shugaban kasar, Talon ya ce rufe iyakar ya jefa mutanen jamhuriyar Benin cikin mawuyacin hali.

A cewar shugaban kasar rufe kan iyakar zai bawa jami’an tsaro damar fitar da wani tsari da zai kawo karshen matsalar baki daya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like