Buhari ya bada umarnin gaggauta fara biyan mafi ƙarancin albashi na ₦30,000


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayar da umarnin gaggauta fara biyan mafi ƙarancin albashi na ₦30,000 ga dukkanin ma’aikatan gwamnatin tarayya da suke karbar albashi kasa da haka.

Shugaban hukumar dake lura da albashi ta kasa, Richard Onwuka Ebule shine ya bayyana a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja.

Ya ce karin zai fara ne tun daga ranar 18 ga watan Afirilu lokacin da shugaban kasa ya amince da sabon tsarin mafi ƙarancin albashin.

Dakta Egbule ya yi karin hasken cewa ma’aikatan da suke daukan albashi kasa ₦30,000 ne ka dai karin ya shafa inda ya ce daga yanzu babu wani ma’aikacin gwamnatin tarayya da zai rika karbar albashi kasa da sabon tsarin albashin daka amince da shi na dubu talatin.

Ya ce za a cigaba da tattaunawa kan yadda karin zai shafi sauran ma’aurata da suke daukar albashi sama da ₦30,000.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like