Buhari ya ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Bikin Dimakwaradiya tare da bawa Abiola lambar yabo ta GCFR


Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar da za a rika bikin murnar Ranar Dimakwaradiya a Najeriya.

Gwamnatin ta bayar da wannan sanarwar a ranar Laraba.Inda ta ce an yi hakane domin girmama marigayi MKO Abiola mutumin da ake zaton ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni shekarar 1993.

Har ila yau gwamnatin ta bawa Abiola lambar yabo mafi girma a kasar ta Babban Kwamandan Askarawan Sojin Najeriya wato GCFR.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kasa Muhammad Buhari ta kuma ce, Babagana Kingibe mutumin da ya yiwa Abiola takarar mataimaki da kuma fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil’adama,Gani Fawehinmi, za aba su lambar girmamawa ta GCON.

Sai dai yunkurin na gwamnatin tarayya ya jawo martani daban-daban.

Ya yin da wasu da dama suke ganin yin haka da shugaban kasa Buhari ya yi abune da ya dace wasu na ganin rashin dacewar haka.

Amma kuma a yankin arewa mutane da dama suna ganin shugaban ya yi hakane domin ya dadawa al’ummar kabilar Yarabawa gabanin zaben shekarar 2019.

Marigayi Abiola ya bayar da gagarumar gudummawa wajen fafutukar kafa dimakwaradiya a kasar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like