Buhari da ministoci 7 za su tafi Afrika ta kudu ranar Laraba


Akalla ministoci 7 ne za su raka shugaban kasa, Muhammad Buhari kasar Afrika ta kudu bisa gayyatar takwaransa na kasar,Cyril Ramaphosa.

Ministocin sune ,Saleh Mamman (wutar lantarki) Rauf Aregbesola(cikin gida) Olamilekan Adegbite(ma’adanai da karafa) Maryam Katagum(karamar ministar ciniki, masana’antu da zuba jari), Bashir Magashi(tsaro) da kuma na harkokin waje, Geoffrey Onyeama.

Abdullahi Umar Ganduje gwamnan jihar Kano, David Umahi na jihar Ebonyi da Simon Lalong na jihar Filato na daga cikin gwamnonin da suke cikin tawagar shugaban kasar da za su bar birnin tarayya Abuja a gobe Laraba.

A wata sanarwa mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya ce Buhari zai tattauna da Ramaphosa kan walwalar yan Najeriya mazauna kasar dama sauran batutuwa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like