Buhari da Atiku sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya


Shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma Atiku Abubakar dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Taron sanya hannu ya gudana ne a cibiyar taro ta kasa da kasa dake birnin tarayya Abuja.

Sauran mutanen da suka halarci wurin taron sun hada da Mahmoud Yakubu shugaban hukumar zabe ta kasa da Abdulsalam Abubakar shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa.

Sakatare Janar ta kungiyar kasashe rainon Ingila, Patricia Scotland, shugaban cocin Katolika shiyar Sokoto,Matthew Hassan Kukah da kuma sauran yan kwamitin na daga cikin mahalarta taron.

Shima tsohon shugaban kasa Yakubu Gawon ya halarci wurin taron domin sanya hannu kan yarjejeniyar.


Like it? Share with your friends!

1
78 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Daukacin Hukumomin Kasannan Fa Su Yi La’akari Da Wassu Kuddurori Da Ake Aiwatarwa. Zamu Iya Sa Kasashen Duniya Su Raina Mana Wayo. Wadda Kuwa, Nigeria Kasa Ce Da Take Tattare Da Daukacin Ma’ilmanta. A Yi Lura Cikin Gudanarwa!

You may also like