Buhari da Aisha sun cika shekaru 30 da aure


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi murnar cikarsu shekara 30 da aurensa da Aisha.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na kafafen sadarwar zamani.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter shugaban yayi addu’ar, Allah ya cigaba da samar da zaman lafiya da kuma albarka a gidansu.

Ita ma mai dakin shugaban kasar,Aisha Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter inda ta ce ta gode Allah da suka shafe shekaru 30 suna tare.

Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan batun inda suka rika yi musu fatan alkhairi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like