Buhari: Baza mu gajiya ba har sai mun ceto ragowar yan matan Chibok


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce gwamnatinsa baza ta gajiya ba har sai ta dawo da ragowar yan matan Chibok da aka sace gida wajen iyalansu.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne cikin wani jerin sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi domin tunawa da ranar da aka sace yan matan shekaru biyar da suka wuce daga makarantar Chibok a jihar Borno.

Ƙungiyar Boko Haram ta sace yan mata 276 daga Chibok cikin watan Afirilun shekarar 2014 a tsawon shekaru 107 ne kacal na yan matan suka dawo gida cikin iyalansu.

Shugaban kasar yace yayi farin cikin ganin irin cigaban da wasu daga cikin yan matan da aka ceto suka samu ta fannin karatu.

“Yau an cika shekaru biyar tun lokacin da aka sace yayanmu na Chibok.Munyi nasarar dawo da 107 daga cikinsu. Amma baza mu gajiya ba har sai dukkanin yan matan sun dawo sun hadu da yan’uwansu. Nayi wannan alƙawarin lokacin da na zamo shugaban ƙasa kuma zan cika shi,” Buhari ya ce

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like