Buhari ba zai fito fili ya bayyana kadararorinsa ba – Femi Adesina


Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ce shugaban kasar ba zai fito fili ya bayyana kadarorin da ya mallaka ba.

Da yake magana lokacin da ya bakunci shirin gidan talabijin na Channels, Adesina ya ce babu wata doka da ta bukaci shugaban kasar ya yi haka a zangon mulkinsa na biyu.

Kungiyar SERAP mai fafutukar tabbatar da adalci da dai-daito ta nemi Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da kuma gwamnoni 36 da su fito fili su bayyana kadarorin da suka mallaka, cikin kwanaki bakwai.

Adesina ya ce fitowa fili a bayyana kadarar da shugaban kasa ya mallaka ba ya cikin doka a bune na kashin kai saboda haka baza a tilasta masa yin haka ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like