Bom ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu biyu a Adamawa


Wani abu da ya fashe kuma ake kyautata zaton bom ne ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu biyu a wata matattarar tsofaffin karafa dake Mubi a jihar Adamawa.

Wakilin Jaridar Daily Trust, ya gano cewa fashewar abun ya faru ne bayan da wasu masu yawon bola suka tsinto wasu karafa inda suka kai wa dillalan ƙarfe dake wurin.

Wani dan kungiyar bijilante dake garin ya ce daya daga cikin yan yawon bola ya mutu nan take ya yin da ragowar mutum biyu suka samu rauni kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa, Abubakar Othman ya tabbatar da mutuwar wani matashi a fashewar abun ya kara da cewa wasu matasan biyu kuma sun jikkata.

Ya ce fashewar ta faru ne a kasuwar yan gwan-gwan dake yankin Kabang a karamar hukumar Mubi ta Kudu bayan da mutanen suka yi kokarin sayar da wani karfe da suka samo.

Othman ya shawarci mazauna garin da su cigaba da gudanar al’amuran su na yau da kullum kamar yadda suka saba, ya musalta jita-jitar da ake yadawa cewa lamarin da yafaru harin kunar bakin wake ne.


Like it? Share with your friends!

1
94 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like